Arsenal za ta sayar da Declan Rice, Tottenham na bibiyar Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images
7 Nuwamba 2025
Kocin Tottenham Thomas Frank na fatan sake haɗewa da ɗanwasan gaban Ingila da Al-Ahli mai shekara 29, Ivan Toney – wanda ya horas a lokacin yana kocin Brentford. (Talksport)
Ɗanwasan gaban Brazil da Real Madrid mai shekara 24, Rodrygo, na cikin jerin ƴanwasan da Tottenham ke nema. (Teamtalk)
Arsenal ta yanke wa ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 26, Declan Rice farashin £132m, bayan Real Madrid ta nuna sha’awar sayen shi. (Fichajes – in Spanish)
Chelsea ta gabatar da tayin ɗanwasan tsakiyar Argentina mai shekara 21 da ke taka leda a Como Nico Paz, amma za ta fuskanci hamayya daga Real Madrid, wadda itama ta ke bibiyar shi. (TBR Football)
Newcastle na tattaunawa da ɗanwasan bayan Netherlands mai shekara 25, Sven Botman kan ƙulla sabuwar kwangila.(Football Insider)
Barcelona ta shirya tattaunawa da Manchester United over a kan sayen ɗanwasan gaban Ingila mai shekara 28 da ke zaman aro a wajen ta, Marcus Rashford. (Teamtalk)
Napoli za ta gabatar da tayi kan danwasan Ingila da Manchester United mai shekara 20, Kobbie Mainoo, a watan Janairu. (Calciomercato – in Italian)
Chelsea da Tottenham da Manchester City da Leeds, Everton da Barcelona da kuma Real Madrid na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Mainoo. (Caught Offside)
Borussia Dortmund na fatan sake sayen ɗanwasan gefen Ingila mai shekara 25, Jadon Sancho, wanda yake zaman aro a Aston Villa daga Manchester United. (Football Insider)
Real Madrid na fatan ɗauko ɗanwasan bayan Faransa da Bayern Munich mai shekara 27, Dayot Upamecano, a kyauta ida kwangilarsa ta ƙare a ƙarshen kakar wasan bana. (Sky Germany – in German)



