‘Mutuwar Gaddafi ta kara kwararowar makamai a Najeriya’: Ministan harkokin waje

- Ministan Harkokin Kasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya yi magana game da rashin tsaro da kwararowar makamai a Najeriya
- Ya ce har yanzu Najeriya na fama da tasirin rikicin da ya biyo bayan kisan Muammar Gaddafi wanda ya ƙara yawaitar makamai
- Tuggar ya karyata zargin cewa an kashe dubban Kiristoci a Najeriya cikin shekaru 10, ya ce alkaluman da ake yadawa karya ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Ministan Harkokin Kasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana damuwa game da karuwar ta’addanci a Najeriya wanda ya yi katutu.
Tuggar ya bayyana cewa Najeriya har yanzu na fuskantar mummunan tasirin rikicin da ya faru bayan kisan shugaban Libya, Muammar Gaddafi.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar yayin taro. Hoto: Yusuf Maitama Tuggar.
Source: Twitter
Tuggar ya musanta cewa ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya a shirin Piers Morgan Uncensored wanda aka wallafa a YouTube.
Kara karanta wannan
Abubuwan da Najeriya ke tattaunawa da Amurka kan barazanar kawo hari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin kisan Kiristoci da ake yi wa Najeriya
Dukan wannan lamari ya biyo bayan zargin da Amurka ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Shugaba Donald Trump ya kira gwamnatin Najeriya da ta kawo karshen wannan matsala tun kafin lokaci ya kure mata.
Trump ya kuma yi barazanar daukar matakin soji idan har gwamnatin ta ci gaba da zuba ido tana ganin abin da ke faruwa a kasar.
Minista ya karyata maganar kisan Kiristoci
Minista Tuggar ya ce maganar kisan Kiristoci a cikin shekaru 10 ba gaskiya ba ne, yana kiran labarin na ƙarya da rashin tabbas.
Ya ce wannan rikici ne ya kawo yaduwar makamai zuwa yankin Arewa da Yammacin Afirka, wanda ya lalata tsaro kuma ya ƙara dagula al’amuran Najeriya.
Tuggar ya ce rahotannin da ke ikirarin kashe mutane 50,000 zuwa 100,000 da rushe coci 18,000 ba masu tushe ba ne, an kuma tabbatar da rashin sahihancinsu.
Kara karanta wannan
Fafaroma Leo ya sanya Najeriya a cikin kasashen da ake tsananta wa kiristoci
Ministan ya kara da cewa Najeriya kasa ce mai kabilu da addinai daban-daban, kuma mafi yawan matsalolin tsaro suna da nasaba da abubuwan da suka faru a Libya.
Shugba Bola Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Getty Images
Abin da ake zargin ya kara ta’addanci a Najeriya
Ya bayyana cewa rugujewar kasar Libya da yaduwar makamai bayan kisan Gaddafi sun taimaka wajen ƙarfafa Boko Haram a yankin tafkin Chadi.
Ministan ya ce gazawar dabarar tsaron Sahel ta Tarayyar Turai ta shafi Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi, inda hare-hare suka kara ta’azzara.
Ya tabbatar cewa duk da kalubalen tsaro, bai dace a fassara su a matsayin kisan kiyashi na addini ba kamar yadda ake yadawa a duniya.
Tuggar ya ce gwamnati na aiki tare da ƙasashe da ƙungiyoyi na duniya domin dakile yaduwar makamai da hana ayyukan tsattsauran ra’ayi.
CAN ta tabbatar da kisan Kiristoci a Najeriya
Kun ji cewa shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya kuma magana kan zargin kisan Kiristoci da ake yi.
Okoh ya ce suna maraba da matakin Amurka na taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro.
Kara karanta wannan
Yar majalisa ta dura kan tsohon shugaban Amurka da ya saukakawa Najeriya kan addini
Kungiyar ta jaddada cewa akwai “kisan ƙare-dangi na Kiristoci” a Najeriya, tana mai cewa CAN ba za ta gajiya ba wajen nema musu adalci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




