Trends-UK

‘Tinubu ya janye su,’ ‘Yan jam’iyyar NNPP 500 sun sauya sheka a Kano, sun bi APC

  • Mutane fiye da 500 daga jam’iyyar NNPP a kananan hukumomin Fagge da Ungogo sun koma APC a jihar Kano
  • Rabiu Bichi ya ce sauya shekar da suka yi ya nuna yadda jama’a ke nuna amincewa da shugaba Bola Tinubu
  • Shugabannin APC sun tabbatar da karbar mambobin da suka shiga jam’iyyarsu tare da cewa za a musu adalci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Mutane sama da 500 daga jam’iyyar NNPP a kananan hukumomin Fagge da Ungogo sun fice daga jam’iyyarsu sun koma APC.

An karɓe su a wani taron da aka gudanar a ranar Laraba karkashin jagorancin shugaban tafkin Hadejia-Jam’are, Rabiu Sulaiman Bichi.

Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Rahoton NAN ya ce taron ya jawo manyan jami’an jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na jihar Kano domin yi wa sababbin mambobin maraba da fatan alheri.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin Bichi yayin karbar ‘yan NNPP

Rabiu Bichi ya bayyana cewa shigar waɗannan mutane jam’iyyar APC ya nuna yadda jama’a ke kara amincewa da jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyya mai mulki.

Ya ce manufofin APC da suka shafi cigaban tattalin arziki, tsaro da noma na jan hankalin ’yan Najeriya daga sauran jam’iyyu.

Bichi ya kara da cewa:

“Za a yi wa sababbin mambobin adalci, za su samu damar shiga ayyukan jam’iyyar kamar sauran tsofaffin mambobi ba tare da wariya ba.”

APC ta yaba da shigar ‘yan NNPP cikinta

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya wakilta, ya yaba da matakin da mutanen suka dauka.

Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Ya ce matakin ya nuna karfin jam’iyyar da kuma yadda manufofinta ke karɓuwa a zukatan al’ummar kasa.

Ungogo ya yaba da manufofin Tinubu

Shugaban jam’iyyar APC a Kano ta Tsakiya, Alhaji Shehu Ungogo, ya bayyana cewa manufofin shugaba Tinubu sun kara habaka tattalin arzikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Bayan murabus daga PDP, ministan Buhari na kokarin ‘hana’ gwamna shiga APC

Vanguard ta wallafa cewa ya ce hakan ya karfafi ’yan Najeriya da kuma tabbatar da cewa APC na kan turbar cigaba da gyara ƙasa.

Ungogo ya ce:

“Jam’iyyar APC ta nuna a aikace cewa tana son kawo sauyi ta hanyar tsare-tsare masu inganci da suka shafi tattalin arziki, noma da tsaro.”

Dalilan sauya shekar ‘yan NNPP a Kano

Wasu daga cikin sabbin mambobin da suka sauya sheka sun bayyana cewa dalilin da ya sa suka koma APC shi ne ganin yadda jam’iyyar ke gudanar da manufofi na cigaban al’umma.

Sun ce jam’iyyar ta nuna kishin kasa da niyyar inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar samar da ayyuka da tallafin noma.

Abba ya yi kira ga ‘yan NNPP a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar NNPP da su kara hakuri da jajircewa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka shirya domin karrama Rabiu Kwankwaso da ya cika shekara 69.

Abba Kabir Yusuf ya ce zai cigaba da aiki tare da Sanata Rabiu Kwankwaso da dukkan ‘yan Kwankwasiyya a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button